ABNA24 : Shugaba Ruhanin, ya ce kasarsa ta shirya sayen riga kafin korona daga kasashen ketare da kuma sarrafa shi a ckin kasar tun bayan da cutar ta bulla.
ya ce shirin da kasar ta yi na karbar riga kafin cutar korona a cikin tsarin nan na COVAX, shi ma ya gamu da cikas saboda matsin lambar tsohuwar gwamnatin Amurka.
Ya kara da cewa wannan ya baiwa Iran, kwarin guiwa na fadi tashin ganin ta samar da kanta riga kafin cutar ta korona, wanda yanzu haka Iran ta yi nisa kan sarrafa riga kafin cutar na kanta.
Yace duk yarjeniyoyin da Iran, ta kulla da kamfanonin na sanya rigakafin basu cimma gacci ba, hatta yarjejeniyar da Iran ta kulla da Indiya na sayan kwalba miliyan 10 na riga kafin kasashe ketare ya cutura sakamakon abunda Indiya ta ce yana da nasaba da matakan shari’a.
A ranar Litini data gabata dai, Iran, ta samu kashin farko na riga kafin cutar ta korona na kamfanin Oxford/AstraZeneca sama da dubu 700 a cikin tsarin nan na COVAX, ta hanyar hukumar lafiya ta duniya (WHO).
342/